Rundunar Yan Sandan Jihar Anambra Ta Kama Yan Fashi Da Makami 11Yan sanda a jihar sun kama yan fashi 11 da suka dade suna addabar al’ummar karamar hukumar Idemili ta arewa da kuma kewayenta. 

Bindigogi kirar gida guda 6 aka gano a wurin yan fashin.

 Sabon shugaban yan sanda da aka tura  Caji Ofis na Ogidi, Mark Ijarafu, ya bayyana haka lokacin da yake mai da martani kan yawan hare-haren da ake kaiwa yan sanda a yankin. 

” Cikin wata daya da nayi a Ogidi, na samu nasarar kama yan fashi  11,bindigogi 6 kirar gida muka kwato daga hannunsu.

“Kodai su bar wannan yankin ko kuma su gamu da gamonsu, munje maboyarsu kuma muna bin sawun wadanda suka kashe Insifecta a Ungunwasike da sauran wurare.

” Wannan wurin bazai dauke mu dasu ga baki daya ba, ya wancin wadanda muka kama an mika su ga sashin yaki da fashi da makami na rundunar yan sandan jihar domin cigaba da bincike.”
  Ijarafu ya kuma yi kira ga al’ummar yankin da su taimakawa rundunar da bayanai akan batagarin da ke yankin. 

You may also like