Rundunar Yan Sandan Jihar Kano Ta Damu Kan Yadda Ake  Samun Rahoton Aikata Fyade Sau 15 A kowace Rana


Yan sanda a jihar Kano sun damu matuka kan yadda suke samun rahoton aikata  fyade sau 10 zuwa 15 a kowacce rana.

 Babban abun damuwarsu shine yawancin wadanda ake yiwa yara ne yayin da masu aikata laifin suke kasancewa manya,a cewar Jumima Ayuba shugabar bangaren dake kula da fyade da kuma sauran laifuka a caji ofis din yan sanda dake shahuci.

” Mun karfi laifin aikata fyade masu sarkakiya a wannan ofishin yan sandan. Mun samu uba da laifin yiwa yayansa na cikinsa su uku fyade.mun kuma samu nasarar kama wani mutum da ya yi wa jaririya yar wata shida fyade, “tace. 

Tace babban dalilin dake kawo matsalar fyade a jihar sun hada da rabuwar aure, tallace-tallace akan tituna,  sakacin iyaye da kuma kai kananan yara aikatau. 

“Dole iyaye su saka ido akan yayansu domin kare su daga cin zarafi,”tace. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like