Rundunar Yan Sandan Kasa Da Kasa Na Neman Maina Ruwa A JalloRundunar ‘yan sandan kasa da kasa wato INTERPOL ta bayyana cewa ta neman tsohon Shugaban kwamitin daidaita tsarin Fansho na kasa, Abdurashid Maina ruwa a jallo bisa zargin cin hanci da rashawa.

Kakakin Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ya ce a halin yanzu hukumomin tsaro na ci gaba da gabatar da rahoton su game da Maina wanda Buhari ya bayar da umarnin korarsa daga aiki bayan an sake dawowa da shi kan aiki ta bayan fage bayan ya jima kasar waje yana kudun hijira sakamakon zargin rashawa da ake yi a kansa.

You may also like