Rundunar Yan Sandan Najeriya Tayi Watsi Da Rahoton Da Yake Cewa Sune Mafi Lalacewa A Duniya RUNDUNAR Yan Sandan Najeriya tayi watsi da rahotan wata kungiyar dake sa ido kan ayyukan Yan Sanda a kasashen duniya, wadda ta bayyana ta a matsayin na karshe cikin jerin kasashen dake iya samar da tsaro ga Yan kasa.Rahotan kungiyar yace Najeriya ce kasa ta 127 daga cikin kasashe 127 da akayi nazari akan su kan yadda ake samar da tsaro da kai dauki lokacin da ya dace, da kuma magance hare haren ta’addanci.

Kakakin rundunar Yan Sandan kasar Jimoh Moshood, ya bayyana rahotan a matsayin yunkurin batawa rundunar suna kan irin nasarorin da take samu da kuma zama ta farko a Afirka wajen gudanar da aikin samar da zaman lafiya a karkahsin Majalisar Dinkin Duniya.

You may also like