Rundunar Yan sandan Ta Musalta Rahoton Garkuwa Da Mutane 20 Akan Hanyar Kaduna Zuwa Abuja  


Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta musalta rahotannin da ake yadawa a wasu kafafen yada labarai cewa mutane 20 ne  akayi garkuwa dasu akan hanyar kaduna zuwa Abuja a ranar Laraba. 

Kwamishinan yan sandan jihar,Mista Agyole Abeh,   ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya kira a Kaduna. 

” Rundunar na sanar da cewa ga baki daya labarin karya ce aka kirkireta domin a jefa tsoro azukatan jama’a.”

Kwamishinan wanda  ya samu wakilcin mataimakinsa Abdulrahman Ahmad ,yace rundunar ta samu rahoton hari kan wasu mutane biyar akan hanyar  Kaduna zuwa Abuja, akayiwa uku daga cikin fashi, biyu kuma akayi garkuwa dasu. 

” Lokacin da rahoton ya samemu tuni muka baza jami’an mu domin ceto mutanen tare da kama wadanda da suka aikata laifin.

” Akan haka babu ta yadda za’ayi  ace,mutane 20 suna tafiya cikin mota daya a sace su ba tare da angansu ba  kuma yan uwansu basu kawo rahoton sacesu ba ko kuma wasu da suka ga abin basu sanar da jami’an tsaro ba. ”

Kwamishinan ya shawarci yan jarida da su tantance labaransu kafin su buga shi. 

Ya kuma shawarci masu amfani da kafar sadarwar zamani da suyi hankali da Labaran da suke yadawa musamman idan basu gamsu da tushen labarin ba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like