Rundunar ‘Yan Sandar Jihar Kano Ta Samu Nasarar Cafke ‘Yan Fashi Da Makami Da Suka Addabi Jama’a Rundunar ‘yansandan jihar Kano tayi holen wasu ‘yan fashi da makami da suke addabar al‘umma da sace sace a ciki da wajen jihar.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar kano, DSP Magaji Musa Majiya ya kira ya bayyana musu cewa a cikin yan fashin sun hadar da masu kwacen motoci, kuma daga cikin su akwai wadanda suka je gidan wata mata suka yi mata fashi sannan suka yi mata fyade.

You may also like