Ruwan Sama Mai Kamar Da Bakin Kwarya Yaci Wani Alaramma Mahaddaccin Al Qur’ani A Gombe


Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya tafi da wani Alaramma mai suna Bello Musa a cikin mota kirar Honda Civic a daren jiya Litinin, bayan ya ja sallar Tarawihi a masallaci.

Marigayi Alaramma Bello shine limamin masallacin gidan Cikaire, kusa da fadar gidan gwamnatin jihar Gombe.

Anga motar a cikin kwarin Kumbiya-kumbiya.

Bayan shafe sama da awa uku ana kokarin ciro Alaramma, an samu cikas na ruwa wanda yake tafiya da karfi cikin kwarin, a karshe an ciro Alaramma amma Allah ya masa rasuwa.

Za a gabatar masa da jana’iza a safiyar yau Talata a masallacin JIBWIS na Bolari a cikin garin Gombe da misalin karfe sha daya na safe idan Allah ya kai mu.

Allah ya jikansa ya gafarta masa. Amin.

You may also like