Ruwan sama ya lalata gidaje sama da 200 a jihar Ekiti


Ruwan sama mai dauke da iska mai karfi ya lalata gidaje sama da 200 cikin watanni biyu na wannan shekara a jihar Ekiti.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar, Jide Borode, wanda ya bayyana haka cikin wata sanarwa da yafitar a Ado Ekiti ranar Litinin inda ya koka cewa akalla kananan  hukumomi uku bala’in ya shafa.

Borode wanda ya koka kan gagarumar illar da ruwan saman ya yi da kuma asarar da mutanen da rufin gidajensu ya buɗe suka yi amma kuma ya lura cewa akwai bukatar a godewa Allah tun da ba a samu asarar rayuka ba a lamarin.
Ya lissafa al’ummomin da abin ya shafa da suka haɗa da, kwaryar birnin Ado,Emure, Ise da kuma Erinjiyan dake karamar hukumar Ekiti ta yamma ya ƙiyasta asarar da aka yi ta kai ta daruruwan miliyoyin naira.

Amma kuma Borode ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kuma hukumar bada agajin ta kasa NEMA da su kawowa al’ummomin da abin ya shafa dauki saboda girman barnar tayi girman da gwamnan jihar baza ta iya tallafawa ita kaɗai ba.

You may also like