Daruruwan magidanta a wurare da dama na Ilorin babban birnin jihar Kwara sun rasa gidajensu sanadiyar ruwa da iska mai karfi da aka dauki tsawon sa’o’i uku ana tsuga shi a ranar Asabar.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa wasu daga cikin gidajen da abin ya shafa iska ta daye rufinsu kuma sun kasance a yankunan da suka fi yawan mutane a birnin.
NAN ya lura cewa kayayyakin da dama mallakar magidantar da suka hada kayan wutar lantarki, kayan abinci , tufafi da sauran kayayyaki masu muhimmanci duk sun kasance a warwatse a wurin da ruwan ya yi barnar.
Wasu daga cikin yankunan da abin ya shafa a birnin Ilorin da kuma kewayensa sun hada da Ganmo, Gaa Saka, Alore Guniyan, Agbooba da sauransu.