Sabbin bayanai a kan kashe tsohon shugaban Amurka John Kennedy.

Asalin hoton, Getty Images

Bayan kimanin shekara 60 da kashe tsohon shugaban Amurka John F Kennedy, an samu wani sabon bayani game da ɗaya daga cikin kisan da ya girgiza Amurkawa a tarihi.

Paul Landis, mai shekara 88 tsohon jami’in keƙen asiri, yana kusa a lokacin da aka kashe tsohon shugaban, ya ce bayan kisan mista Kenedy shi ne ya ɗauki harsashin da aka harbe shi da shi daga cikin motar tsohon shugaban, sannan ya ajiye shi kan gadon da ka ɗauke shi zuwa asibiti.

Wannan bayani tamkar ya makara a irin wannan batu da ya shuɗe tun shekarun 1960, to amma ga mutanen da suka shafe gomman shekaru suna neman hujjoji dangane da kisan tsohon shugaban, wannan sabon bayani na mista Landi wata babbar makama ce a gare su.

An samu hujjoji masu yawa kan irin hadin bakin da waɗanda ke da hannu, da wanda ya ɗauki nayin kashe shi, da yawan alburusan da aka harbe shi, tun lokacin da aka yi kisan gomma shekaru da suka wuce.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like