Kason farko na malaman makarantun da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka za su fara aiki a watan Fabrairu.
Jami’an Hukumar Bada Ilimi tun Daga Tushe ta SUBEB sune suka bayyana haka lokacin da suke sanar da gwamna Nasir El-Rufai cigaban da aka samu a shirin daukar sabbin malaman.
Jami’an na SUBEB sun tabbatarwa da gwamnan cewa tuni aka kammala duba jarrabawar da aka yi wa sabbin malaman da za’a ɗauka. Inda suka tabbatarwa da gwamnan cewa kason farko na malam za su fara aiki a tsakiyar watan Faburairu.
El-Rufai ya gana da shugabannin kananan hukumomi 23 da kuma sakatarorin iliminsu.Inda ya karbi rahoton halin da makarantu ke ciki a dukkanin kananan hukumomin.
A cewar mai magana da yawun gwamnan Samuel Aruwan, shugabannin kananan hukumomin sun bada rahoton cewa yawancin malaman Kaduna sun je aiki inda suka yi kunnen uwar shegu da yajin aikin da kungiyar malamai ta kasa NUT ta kira.
NUT ta nemi malaman sun zauna domin nuna adawar su da shirin gwamnati na korar malamai 20,000 da tayi.