Sabbin Takardun Naira: A Tsawaita Wa’adi Da Shekara GudaGwamnonin Jihohin Najeriya 36 sun ba Babban Bankin Najeriya shawarar ya kara wa’adin daina amfani da tsoffin takardun kudin naira zuwa shekara daya nan gaba, a daidai lokacin da wasu Jihohi da kananan hukumomi suke karbar tsofin kudin. Amma kwararru a fannin tattalin arziki na ganin kara wa’adin shi ne mafi dacewa a halin yanzu.

Wannan shawarar da Kungiyar Gwamnonin Najeriya suka bayar ta biyo bayan wani zama na musamman ne da ta yi da Shugaba Muhammadu Buhari, kamar yadda mai magana da yawun Kungiyar, Abdulrazak Bello Barkindo, ya shaida wa Muryar Amurka ta wayar tarho.

Razak ya ce Gwamnonin sun nuna goyon baya ga matakin sauya kudin Najeriya da ake ganin ya dauki dogon lokaci ba a yi, amma kuma suna ganin lokacin aiwatar da tsarin ne bai yi daidai ba.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele

Razak ya ce Gwamnonin sun nuna rashin jin dadinsu da irin wahalhalun da ‘yan kasar ke fuskanta, inda suka ce duk da tabbacin da Ministan Shari’a ya bayar cewa Gwamnati za ta bi umurnin Kotun Koli al’amarin sai kara tsannanta ya ke, saboda haka suna ganin gara a dauki mataki na gaggawa saboda kar a yi wa tattalin arzikin kasar illar da ba za a iya jurewa ba.

Amma ga Kwararre a fanin tattalin arziki na kasa da kasa, Shuaibu Idris Mikati, ya bada misalai da yadda sauran kasashe suke sauya kudadesu inda ya yi fatan za a bi wannan tsarin.

Sabbin kudin Naira

Sabbin kudin Naira

Mikati ya ce Kasashe irinsu Indiya da Rasha da China da Ingila da Zimbabwe duk sun sauya kudadensu amma ba a samu matsaloli ba saboda ba su yi wa lokacin canjin wa’adi ba. Mikati yana mai ganin bin irin wannan tsarin ba zai haifar wa tattalin arzikin kasar da mai ido ba.

To saidai a Karamar Hukumar Mangu ta Jihar Filato Alhaji Dauda Abubakar ya shaida wa Muryar Amurka cewa ana ta mu’amala da tsofaffin kudaden saboda babu sabbin. Abubakar ya ce a karamar hukumar Mangu ana bin umurnin da Kotun Koli ta bayar ne, tare da fatan mahukunta ba za su bari kudaden mutane su salwanta ba. Abubakar ya ce suna fata bankin CBN zai zo ya karbi tsoffin kudaden sannan a ba su sabbabi.

Gobe Laraba ne Kotun Koli za ta yi zama na musamman akan karar da Jihohin Kaduna, Kogi, Zamfara da Neja suka shigar akan batun karancin sabbin Kudaden.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like