Sabbin ‘yan wasa 16 ne suka fara yi wa Chelsea wasa a bana



Enzo Fernandez

Asalin hoton, Getty Images

Kimanin ‘yan wasa 16 suka yi Chelsea wasa a karon farko a kakar 2022/23.

Kenan an doke tarihin ‘yan kwallo sabbi da yawa da suka yi mata tamaula a karon farko a tarihin da aka kafa a kungiyar a 1909.

Sabbin ‘yan wasa Enzo Fernandez da Noni Madueke, wadanda suka buga karawar da Chelsea ta tashi 0-0 da Fulham a Premier suka cika 16 jimilla a bana.

A kakar da ‘yan wasa da dama da suka fara buga wa Chelsea kwallo ita ce a 1905/06, sune wadanda suka fara yi mata tamaula.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like