Sabon Fada Ya Kara Barkewa A Jihar NejaLabarin da muke samu a yanzu haka na tabbatar da cewar fada ya barke tsakanin wasu matasa da jami’an tsaro na ‘yan banga a unguwar Tukura dake Kontagora Jihar Neja, inda ‘yan bangan suka kara harbin wani matashi da bindiga.

A ranar Alhamis din wannan makon ne rikici ya barke tsakanin matasa da jami’an tsaro na ‘yan banga a garin Kontagora wanda yayi sanadiyyar rasa ran mutum biyu da jikkata mutane uku ciki harda mace guda.

You may also like