Sabon kawacen adawa da Macky Sall a Senegal | Labarai | DWAn gudanar da taron kaddamar da hadakar da aka yi wa lakabi da ”Mouvement des forces vives du Sénégal” watau F24 a ranar Lahadi 16.04.2023 a birnin Dakar fadar gwamnati, kuma taron ya samu halartar shugabannin jam’iyyun adawa da na kungiyoyi fafitika ciki har da madugun adawan kasar Ousmane Sonko.

Babbar kokowar da ke gaban hadakar ta F24 wacce jam’iyyu da kungiyoyi 120 suka saka hannu a takardunta ita ce ta ganin shugaba Macky Sall wanda ya dare gadon mulki bayan lashe zabukan 2012 da 2019 ya mutumta kundin tsarin mulkin kasar wanda ya haramta masa tsayawa takara a karo na uku.

Senegal dai da a shekarun baya ake misali da ita a Afirka kan mutumta dimokuradiyya ta fada cikin rikicin siyasa ne tun lokacin da shugaba mai ci Macky Sall ya kaddamar da dirar mikiya kan masu neman kawo masa cikas kan yunkurinsa na neman mulki a wa’adi na uku a zabukan kasar na 2024.

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like