Sabon Rikici Ya Ɓarkewa APC


Sabon rikici na neman barkewa a jam’iyyar da ke mulki ta APC bayan da mataimakan Shugaban jam’iyyar su shida na shiyya shiyya sun fito fili sun nuna adawa da salon jagorancin Shugaban jam’iyyar na Kasa, Cif John Odigie-Oyegun.

A cikin korafin da suka gabatar, Mataimakan Shugaban sun zargi Shugaban jam’iyyar da rashin adalci, kashe kudaden jam’iyya ba bisa ka’ida ba sannan kuma yana tafiyar da harkokin jam’iyyar a bisa son ransa wanda a cewarsu hakan, zai rage kimar jam’iyyar a idon duniya.

You may also like