sabon shirin samar da takin zamani a Najeriya


Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani sabon shirin tallafawa manoma da taki wanda zai kai ga samar da taki ton 4,000 a makon farko dan tallafawa manoman.

Shi dai wannan shiri da shugaba Muhammadu Buhari ya amince da shi a watan Disamba, zai taimaka ne wajen samar da ton miliyan 1 na takin NPK wanda za’a sayarwa manoma akan kudi naira 5,500 sabanin farashin N8,000 da ake sayarwa yanzu haka.

kungiyar manoma ta kasa ta bakin Sakatare kungiyar sakamakon nasarar noman da aka samu, yanzu haka mutane da dama sun rungumi noman rani.

You may also like