Sabon shirin taimakawa yan gudun hijira a Turai


 

Ministocin kasashen Faransa,Jamus da na Fologne sun shigar da kira zuwa kungiyar tarrayar Turai don samar da wani shiri na kai dauki zuwa yan gudun hijra.

Shirin zai mayar da hankali ne wajen yi amfani da sauren cimaka irin su danyen nama da ya rage daga cikin wanda ake amfana da shi a kasuwanin turai.
Stephane Lefool Ministan noman kasar Faransa ya jadada aniyar hukumomin Faransa wajen samar da kayakin marmari koda kalilan ne zuwa yan gudun hijira dama wasu mabukata a yankunan dake fama da yaki.

Masu lura da siyasar a yankin na turai sun yaba da wannan sabon salo duk da yake hukumomin ba su bayar da na su amincewa ba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like