Sabon tsarin ciyar da ‘yan gudun hijirar Boko Haram


 

 

Fito na fito da ‘yan gudun hijirar Boko Haram suka yi a Maiduguri kan zargin karkatar da abincin tallafin da ake basu ya sanya gwamnati sake lalle na basu abincin a hannunsu.

 

Daukar sabon salon da batun matsaloli na rashin wadataccen abinci ko karancin abinci mai gina jiki a sansanonin mutanen da suka rasa mauhallansu a jihar Borno ya sanya fuskantar fito na fito a tsakanin mahukunta da mutanen da ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira. Fuskantar irin wannan matsala da ke sanya nuna ‘yar yatsa ga jami’an da ke kula da lamuran wadannan bayin Allah ya sanya gwamnatin jihar Borno sake lalle a kan tsarin rabawa mutanen abinci.

Flüchtlingslager in Bama, NigeriaNan gaba ‘yan gudun hijira za rika dafawa kansu da kansu abinci don gudun samun matsala

Mallam Ahmed Satomi da ke zaman shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Borno ya ce mutanen da suka rasa muhallan nasu dai sun yi koke karancin abinci da ya sanya su kaiga fito na fito da gwamnati don neman mafita daga wannan matsala. A yayinda ake ci gaba da tirka-tirka a kan wannan batu, kungiyoyi masu zaman kansu na ci gaba da zarya zuwa Maiduguri domin talafawa ga wannan babban kalubale da ke fuskantar Najeriya na gaza kulawa da mutanen da suka rasa mahalansu.

Yanzu haka dai da dama musamman masu sanya ido kan abubuwan da ka je su koma na dakon ganin irin tasirin wannan sabon tsari da gwamnatin ta bullo da shi don shawo kan wannan matsala daidai lokacin da kungiyoyin kasa da kasa ke kara nuna ‘yar yatsa a game da matsalar karancin abinci mai gina jiki da ke mumunar illa ga yara kanana da matsalar ta shafa.

You may also like