Sabuwar Cutar MonkeyPox Ta Bazu Zuwa Akwa Ibom Da RiversSabuwar cutar nan ta ‘Monkeypox’ wadda ta samo asali daga jihar Bayelsa, a halin yanzu ta fara yaduwa zuwa jihohin Akwa Ibom da Rivers, lamarin da ya janyo zaman fargaba a wadannan jihohi.

Ita dai wannan cuta ta ‘ Monkeypox’ Likitoci sun ce Birai, Beraye da dabbobi ne ke kawo wannan cuta sannan sun bada shawarar cewa mutane su yi hankali da dabbobi musamman irin na daji, bera da Birai.

Har yanzu kuma ba a samu maganin ita wannan cutar ba amma kuma masana kiwon lafiya sun jaddada cewa Rigakafin cutar shi ne, mutane su Yawaita wanke hannayensu da kuma takaita yin masabaha da juna.

You may also like