Majalisar dokokin jihar Gombe ta dakatar da wakilan ta guda hudu da suka fito daga jam’iyar APC har na tsawon kwanakin zaman majalisa hudu.
Matakin ya biyo bayan zargin da ake musu na taka rawa lokacin da wani wakili a majalisar ya sace sandar majalisar a zamanta na ranar Alhamis.
Majalisar ta kuma nemi kwamitin da ta kafa da ya binciko yadda lamarin ya faru kana ya bada rahotonsa a ranar Litinin.
Shugaban masu rinjaye a majalisar, Fabulous Amos, shine ya bayyana haka lokacin da yake wa manema labarai karin bayani kan lamarin da ya faru.
Ya ce mambobin da aka dakatar sun dauke sandar majalisar ya zuwa wani wuri da ba a sani ba lokacin da majalisar take tsaka da zama, ba tare da izini ba.
Amos ya bayyana sunayen wakilan da aka dakatar da suka hada da Abdullahi Abubakar, Mohammed Bello, Ibrahim Sadiq Abubakar and Walid Mohammeda