Majalisar kasa ta gayyaci sanata Ovie Omo-Agege da kuma sanata Ali Ndume kan zargin da ake musu na taka rawa wajen sace sandar majalisar dattawa.
A ranar 18 ga watan Afirilu, Omo-Agege ya isa majalisar dattawa tare da wasu mutane da ake zargin yan daba ne inda suka sace sandar majalisar wacce itace alamar ikon da majalisar take da shi.
Ana zargin Ndume da hana dan sandan dake daukar sandar ya bawa sandar kariya a lokacin da ake kokarin sace shi.
A lokacin da lamarin ya faru majalisar ta bawa rundunar yan sanda wa’adin sa’o’i 24 domin su nemo sandar inda suka samu nasarar lalubo sandar a washegarin ranar.
Majalisar dattawa da ta wakilai sun kafa wani kwamitin hadin gwiwa karakashin shugabancin, Bala Na-Allah domin ya binciko yadda lamarin ya faru.
Ya yin zaman kwamitin Na-Allah ya ce dole mutanen biyu su kare kansu daga zargin da ake musu ta hanyar bayyana a gaban kwamitin.