Saka Rigar Barcelona Mai Dauke Da Alamar Kamfanin Jiragen Sama Na Qatar Zai Jawo Daurin Shekaru 15 A Kasar Saudiya Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da suka saka rigar kungiyar mai dauke da alamar tallan kamfanin jirgin sama na kasar  Qatar zasu iya fuskantar dauri na tsawon shekaru 15 da kuma tarar €135,000 kimanin naira miliyan 60 a kudin Naira. 

 Sabuwar dokar ta biyo bayan katse duk wata dangantaka da kasashen, Saudiya, Masar, Bahrain da Kuma Imarat wato hadaddiyar daular larabawa sukayi da kasar Qatar. 

 Kasashen dai na zargin kasar Qatar da goyon bayan yan ta’adda da kuma hada kai da kasar Iran.  

Yarjejeniya tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da kuma kamfanin jiragen sama  na Qatar zata kare ne a  karshen watan Yunin wannan shekarar da muke ciki. 

Kasar Saudiya dai ta rufe kan iyakarta da Qatar tare da dakatar da duk wata harkar sufuri har ta jiragen sama. 

You may also like