
Asalin hoton, OTHER
A Najeriya, dan takarar gwamnan jihar na babbar jam’iyyar hamayya ta PDP, a zaben da ya gabata, Sanata Yakubu Lado Dan Marke, ya yi watsi da sakamakon zaben da hukumar zabe ta bayyana.
Cikin wata hira da ya yi da BBC, Sanata Lado, ya ce, zabe ne mai cike da magudi, da aringizon kuri’u, da barazana ga masu zabe, da dai duk wani ha’incin da bai taba gani a harkar zabe ba.
Ya ce,” Ba mu gamsu da wannan sakamakon zabe ba tun da mun san ba abin da al’umma suka zaba bane aka bayyana.”
Dan takarar gwamna na jam’iyyar ta PDP, ya ce, yakamata a daina yin zabe kawai a rinka yin nadi, don yana ga hakan ya fi alkhairi.
Ya ce,” Zaben da ake yaudarar mutane ne kawai ake ana kuma bata musu lokaci.”
Sanata Lado Dan Marke, ya ce “‘Yar manuniya ta nuna ko a lokacin yakin neman zabe, domin duk inda jam’iyyar APC ta je kampe bata ji da dadi saboda mutane sun gaji da ita, amma mu duk inda muka je maraba ake damu.”
Dan takarar gwamnan na babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a Katsinan, ya ce a zaben shugaban kasa ai an ga abin da ya faru, suna kan Mulki amma sai da muka kada su.
Ya ce,” Idan aka lura ai za a ga cewa mutane a Katsina ba su fito zaben gwamna sosai ba, saboda haushin abin da aka yi musu a lokacin zaben shugaban kasa, saboda abin da suka zaba ba shi aka basu ba.”
Sanata Lado, ya ce, “ Babu kunya ba tsaron Allah aka ninka kuri’u don kawai su samu nasara, wanda kuma kowa ya san cewa a zaben gwamna sam mutane basu fito sosai ba.”
Y ace, don haka wannan sakamakon zabe ba zabin jama’a bane zabi ne na wasu mutane da suka zauna suka rubuta abin da suke so.
Dan takarar gwamna a jam’iyyar ta PDP a Katsinan, ya ce, “ Gaskiya zata bayyana, domin muna wannan gwagwarmayarne ba don kanmu bas ai don al’ummar jihar Katsina.”
Ya ce, su ba zasu yi wani abu da zai sabawa doka ba, zasu yi abin da doka ta tanada, mutane su kwantar da hankulansu za a yi duka abin da ya dace don kwatowa al’ummar jihar katsina hakkinsu.