Sakataren Gwamnatin Tarayya Ya Wanke Kansa Bisa Umarnin BuhariSakataren a Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal ya wanke kansa bisa zargin da majalisar tarayya ta gabatar a kansa bisa yadda ya ba kamfaninsa kwangilar cire ciyawa a sansanin ‘yan gudun hijira a kan Naira milyan 200.
Ministan Shari’a ne dai ya nemi Babachir ya wanke kansa kamar yadda aka umarci Shuganban Hukumar EFCC , Ibrahim Magu bisa umarnin Shugaba Buhari. A halin yanzu dai Shugaban ake jira ya yanke shawara game da makomar wadannan manyan jami’an gwamnatinsa.

You may also like