Sakataren gwamnatin tarayya ya ziyarci Ekwueme a wani asibiti dake London


Boss Mustafa, Sakataren gwamnatin tarayya ya ziyarci tsohon mataimakin shugaban kasa a lokacin mulkin  shagari, Alex Ekwueme wanda ke jinya a wani asibiti dake a birnin London.

Ekwueme wanda ya shafe makonni biyu yana fama da rashin lafiya an dauke shi zuwa Birtaniya a ranar Lahadi.

Shugaba kasa Buhari ne  ya bada umarnin a fitar dashi zuwa kasar waje bayan da akayi masa bayanin halin da tsohon mataimakin shugaban kasar yake ciki.

” Umarnin ya haɗa da ɗaukar shatar jirgin ɗaukar marasa lafiya da kuma kuɗin da za a kashe wajen yi masa magani shugaban yayi addu’ar Allah bashi lafiya, ” Garba Shehu mai magana da yawun shugaban kasa yace.

A wani sakon da gwamnatin tarayya ta wallafa a shafinta na Twitter, gwamnatin tace sakataren gwamnatin tarayyar ya kuma isar da sakon fatan alkhairi daga shugaban kasa Buhari ga marar lafiya.

You may also like