Sakataren Gwamnatin Tarayya Yayi Raddi Ga Majalisa Bisa Zargin Karkatar Da Kudaden Arewa Maso GabasSakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal ya mayar da raddi ga majalisar Dattawa wadda ta nemi a cire shi tare da hukunta shi bisa zargin karkatar da kudaden jin kai na yankin Arewa maso gabas inda ya bayyana zargin a matsayin wata makarkashiya na neman bata masa suna.
Tun da farko ne dai, majalisar Dattawa ta nemi a tuhumi Sakatare gwamnati bayan ta karbi rahoton binciken kwamitin da ta kafa don tantance yadda kwamiti Shugaban kasa kan samar da kayan Jin kai ga jihohin da rikicin.

 Boko Haram ya shafa inda rahoton ya gano yadda Sakataren gwamnati ya ba wani kamfaninsa kwangilar cire ciyawa a wani sansanin ‘yan gudun hijira a kan kudi Naira milyan 200.

You may also like