Sakataren Kungiyar CAN Ya Mutu


Sakataren Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, Rabaran Musa Asake ya mutu.

An ce Asake ya mutu a Abuja bayan gajeriyar rashin lafiya.

Jonathan, kaninsa wanda wakili ne a majalisar wakilai, ya tabbatarwa da jaridar Punch mutuwarsa.

“Ya mutu da safiyar yau yanzu haka muna dakin ajiye gawarwaki.Ina tare da shi jiya(Alhamis a gidansa,”ya ce.

Adebayo Oladeji, mai taimakawa shugaban kungiyar CAN kan harkokin yada labarai ya ce kungiyar zata fitar da sanarwa anan gaba.

Shugabancin kungiyar na jihohin Arewa 19 ya bayyana kaduwarsa,kan faruwar lamarin, ya mutu lokacin da mutane da kuma cocin ke bukatar mutum irinsa wanda yake tsayawa akan gaskiya.

Mutuwar ta Asake na zuwa ne kasa da mako biyu bayan da ya jagoranci zanga-zanga kan kashe-kashen dake faruwa a kasarnan.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like