Sakataren tsaron Amurka na ziyara a Ukraine – DW – 11/20/2023kan yakin da take da Rasha

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagone ta fidda ta ce a yayin wannan ziyara da ba a sanar da ita ba tun da farko saboda dalilai na tsaron, babban jami’in Lloyd Austin zai gana mahukuntan Ukraine domin tabbatar musu da cewa taimakon da Washington ke bai wa kasar a fannin tsaro zai dore har sai ta kubuta daga mamayar Rasha.

Karin bayani:  Amurka ba za ta yi watsi da Ukraine ba

Ziyarar jami’in dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Joe Biden ke shan suka daga ‘yan Replublicain kan ci gaba da tallafa wa Ukraine a kan yakin da take da Rasha, sai dai amma shugaban na dage wa kan cewar idan har Washington ta ja da baya to shugaba Vladimir Putin zai ci gaba da cin karensa ba bu babbaka.

Karin bayani:  Ziyarar Kim ga Putin ta sa Amurka fargaba

A baya-bayan nan dai a yayin wata hira da manema labarai shugaba Volodymyr Zelensky ya tabbatar da cewa fadan da ake gwabza wa a zirin Gaza ya kawo tseko ga tallafin makaman da sojojin kasarsa ke samu, lamarin da bayyana a matsayin abun damuwa.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like