An Sake Daga Zamen Shugaban Kasa A Kasar Somalia Saboda Matsalolin Tsaro


 

Hukumar zabe a kasar Somalia ta bada sanarwan dage zaben gama gari na kasar zuwa wani lokaci.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa hukumar zaben kasar ta bada sanarwa a safiyar yau Talata kan cewa an dage zaben zuwa wani lokaci nan gaba. Bayanin ya kara da cewa, duk da cewa ba’a sanya wata rana ba amma tabas za’a gudanar da zaben kafin karshen wannan shekara.

Wannan shi ne karo na ukku da ake nage zaben gama gari a kasar ta Somalia. Da farko dai an shirya gudanar da shi ne a cikin watan Augustan da ya gabata, sannan aka dage. Dagewar dai yana sanya fargaba kan ingancin zaben ga al-ummar duniya. Jakadan majalisar dinkin duniya na musamman a kasar ta Somalia Mr Michel Kiting ya fadawa masu neman labarai kan cewa yana sanya tababa a cikin zukatan kasashen da suke tallafawa kasar.

You may also like