An sake dage zaben Somaliya


Hukumomi a Somaliya sun sanar da sake dage zaben ‘yan majalisun da aka shirya farawa a wannan Lahadin

An dai ba da dalilai na tsaro a matsayin abin da ya sanya aka dage zaben na ‘yan majalisun dokoki. Wannan dai shi ne karo na biyu cikin makonni takwas din da suka gabata da aka dage zaben kasar. Gabannin fara zaben da aka shirya yi a yau, ‘yan kungiyar Al-Shabab sun umarci magoya bayansu da su kai farmaki kan dukannin wurin da aka kebe don gudanar da zabe. Ya zuwa yanzu dai hukumomi ba su kai ga sanya sabuwar rana ta yin wannan zaben ba.

You may also like