Sake dawo da martabar Turai a siyasance


2016-09-15t105108z_705594274_lr1ec9f0u4y5q_rtrmadp_3_france-germany

 

Faransa da Jamus na kokarin ganin sun sake dawo da martabar kungiyar tarrayar Turai,hakan dai na zuwa ne bayan da Francois Hollande Shugaban Faransa yayi wata ganawa da waziriyar Jamus Angela Markel a yau alhamis a fadar l’Elysée dake birnin Paris.

Shugabanin biyu sun yi kira ga takwarorinsu na kasashen turai 27 da ke shirin gudanar da taro a gobe juma’a a Bratislava domin samar da ingantacen tsari na kungiyar tarayyar turai da ya tsinci kansa cikin mawuyacin hali sakamakon ficewar Britaniya daga cikin kungiyar.
Kasashen turai za su futar da wani sabon tsari na sake dawo da martabar Turai a Duniya don magance matsallolin dake gaf da mamaye yankin.

You may also like