Sake Fasalin Naira Zai Yi Illa Ga Talakawa Da Kananan Yan Kasuwa
Babban Bankin Duniyan ya yi gargadi cewa sabon kudin na iya yin illa ga harkokin tattalin arzikin talakawan kasar da ma kananan masana’antu saboda gajeren lokacin da bankin Najeriya ya diba domin sauya tsofaffin kudaden zuwa sabbi.

Bankin Duniya wato World Bank mai Shelkwata a Washington DC ya bayyana gargadin a wani sabon rahoto ne da ya fitar a shafinsa na yanar gizo mai dauke da suna Nigeria Development Update a turance.

Bankin Duniya ya nuna cewa sabuwar manufar za ta iya yin illa ga kanana yan kasuwa musamman masu hada-hadar kudi na yau da kullum da kuma kananan masana’antu. Wani abu da kwararre a fannin tattalin arziki na kasa da kasa Shuaibu Idris Mikati ya ce gargadin da Bankin Duniya ya yi ba sabon abu bane.

Mikati yace Bankin Duniya na bada irin wannan shawarwari ga kasashe ko masu tasowa ko kasahen Turai wadanda suka riga suka cigaba.

Mikati ya ce wannan shawara ce aka bayar akan illoli da ka iya tasowa kan wannan sauyin launin wasu kudade da Bankin Najeriya ya yi.

Mikati ya ce wannan shawara ce da ya kamata a duba domin ana cewa yan Najeriya sun kai miliyan 220 amma in an duba wadanda suke hulda da banki wadanda suke da lambar ajiya wato BVN, ba su wuce miliyan 60 ba.

Saboda haka wannan ya nuna cewa masu ajiya a bankuna ba su da yawa sosai. Mikati ya ce abu ne da Bankin Najeriya ya kamata ya duba saboda ya dauki mataki kaman yadda ya saurari koken mutane, wajen kara yawan kudin da za a cire a asusun bankuna.

Shi kuwa mai nazari a fanin tattalin arziki Yusha’u Aliyu ya yi tsokaci cewa tsarin yana da kyau amma ya kamata a fara shi daga manyan birane

Yasha’u ya ce Babban Banki yana da dama da zai gudanar da wannan tsari amma ya kamata ya yi la’akari da irin mutanen da ya kamata su yi amfani da tsarin musayar kudi ta dandalin yanar gizo wadanda yawancin su suna kauyuka ne kuma ba sa jin turanci balle su iya amfani da dandalin yanar gizo wajen mu’amala da kudi.

Yusha’u ya ce Babban Bankin Najeriya ya duba yadda zai yi gyara a wannan fannin domin ya kara yawan lokaci da za a iya musayar tsofaffin kudaden zuwa sababbin Kudade idan ba haka ba zai kawo rudami a harkar farfado da tattalin arzikin kasar ba ki daya.

Akan haka ne gagarabadan Majalisar Wakilai Mohammed Tahir Monguno ya sha alwashin tada maganar karin lokaci da ma ta wayar da kan al’umma musamman na Jihohin Borno da Yobe idan majalisa ta dawo daga hutun karshen shekara. Monguno ya ce yawancin kauyuka ba su da bankuna, kuma mutane dayawan gaske ba su da ilimin amfani da wayoyin su wajen mu’amalar kudi, gashi kuma ba kullum ake samun hanyoyin sadarwa ba.

Munguno ya ce zai dage har sai ya ga an samu sauyi a lokaci na yin chanjin kudaden.

Abin jira a gani shi ne irin matakin da Babban Bankin Najeriya zai dauka ganin cewa Bankin Duniya da ma yawancin yan kasa sun nemi a kara tsawon lokaci saboda a samu a sauya tsofaffin kudaden ba tare da an musguna wa kowa ba.

Saurari rahoton Madina Dauda:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like