An Sake Kai Hari A Kudancin Kaduna


elrufai-kaduna

An kai hari akan al’ummar Asso dake ƙaramar hukumar Jema’a dake kudancin jihar Kaduna.

Haryanzu dai babu cikkakkun bayanai kan yadda harin yafaru da kuma irin asarar rayuka da dukiya da akayi tuni gwamnan jihar Mal Nasir El-Rufa’i yayi Allah wadai da harin ta bakin mai magana da yawunsa Mista Samuel Aruwan.

Harin kan al’ummar Asso ana ganinsa a matsayin cigaba da rikicin da yaƙici yaƙi cinyewa tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma ƴan asalin yankin na kudancin Kaduna.

Gwamna El-Rufa’i yayi ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu kana ya jajantawa waɗanda suka samu raunuka, yayin da yaƙara tabbatar da tsaurara matakan tsaro don kawar da ƴan ta’addan dake cikin dazuzzukan yankin.

Gwamnan ya kuma ƙaddamar da wani shirin samar da tsaro da akewa laƙabi da ‘Operation Harbin Kunama II’ da zai taimakawa jami’an soja wajen kawar da mutanen dake ɗauke da makamai a yankin.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like