An kai hari a Masallacin Juma’a na garin Dresden wanda Hukumar Diyanet ta Turkiyya ta gina.
An kai harin ne da misalin karfe goma na daren Talatar nan inda aka ji wata babbar kara a cikinsa.
Na’urar nadar bayanai da ke gurin ta dauki hotunan yadda al’amuran suka faru.
Wani mutum ne ya jefa wata kwalba mai dauke da iskar gas wadda a kofar gidan limamin Masallacin.
Bayan kai harin wuta ta kama a Masallacin wanda jama’a makota suka yi kokarin kashewa.
Jakadan Turkiyya a Jamus Ahmet Bashar ya shaida cewa, babu wani da harin ya shafa.
Tuni jami’an tsaro suka fara bincike don kamo maharin.