Kungiyar “National Association of Nigerian Students dake Uganda, suna kira ga Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kuma Babban Bankin Kasa (Wato Central Bank of Nigeria). Akan a dubi halin tsadar rayuwa da da ‘yan asalin Nijeriya dake karatu a kasashen waje suke ciki dalilin zoben da aka sanyawa katin ATM din duk wanda ke wajen Nijeriya.
Hakika rashin samun damar amfani da katin ATM ba karamar barazana ba ce ga wadannan dalibai ‘yan asalin Nijeriya dake karatu a waje, domin wannan zai sanya da yawa daga cikin masu karatu a wajen Nijeriya su rasa gurabun karatunsu dalilin rashin samun damar fitar da kudi domin biyan kudin karatunsu.
Yanzu haka wasu daga cikin Makarantu suna gab da hana ‘yan Nijeriya shiga aji domin daukar darasi dalilin rashin biyan kudin makaranta da ba su yi ba.
Haka kuma gidajen da ‘yan Nijeriya suke haya babu kudin biyan haya dalilin rashin samun damar fitar da kudi daga asusun ajiyarsu su biya. Wannan ya sa wasu daga cikin masu gidajen (na haya) suka bawa da yawa daga cikin dalibban lokaci domin su biya su ko kuma su bar musu gidajensu.
Abu na uku daga cikin matsalolin da muke fuskanta kuwa shine, rashin abinci domin da yawa daga cikin dalibai ba su da abincin da za su ci dalilin rashin samun damar fitar da kudin dake asusun ajiyarsu.
A kan haka Wannan Kungiya ta “National Association of Nigerian Students dake Uganda” take kira ga Gwamnatin tarayya da Babban Bankin Nageriya da duk masu fada aji akan su duba akan wannan lamari domin a shawo maganin wannan matsala ta rashin amfani da katin ATM a kasashen Waje. Saboda gudun fadawar ‘yan asalin Nijeriya cikin wani kazamin yanayi (Na sace-Sace ko karuwanci) wanda bama fatan hakan ta faru (Allah ya tsare).
Muna fata da rokon duk wanda ya samu wannan sako zai taimaka ya isar mana da shi duk inda ya kamata domin wannan matsalar ta zamo tarihi. Sannan muna godiya ga Jaridar RARIYA akan taimakon da take mana.
Sako daga;
Muhammad Giyas Ibrahim
Vice president Academics affairs of National Association of Nigerian Students in Uganda