Sakon Sabuwar Shekarar 2017 Daga Shugaba Buhari Zuwa Ga ‘Yan Nijeriya


buhari

 

A sakonsa ga al’ummar Nijeriya na sabuwar shekarar 2017, Shugaba Muhammad Buhari ya nemi kungiyar Shi’a da na kungiyoyin tsagerun Niger Delta kan su rungumi zaman lafiya tare da bin dokokin kasar a yayin da aka shiga sabuwar shekara.

Buhari ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bin hanyoyin yin sulhu da wadannan kungiyoyin inda ya sake rokon mayakan Niger Delta kan su daina fasa bututun mai, su zo a zauna kan teburin zaman lafiya.Ya kuma nemi jami’an tsaro kan su rika mutunta wadannan kungiyoyi a duk lokacin da wata rigima ta hada su.

Haka nan kuma Shugaba Buhari ya jaddada cewa dole ‘yan Nijeriya su zauna da junansu cikin mutunci da girmamawa yana mai cewa wadannan rukunai biyu ne kadai za su tabbatar da ci gaba da zaman Nijeriya a matsayin dunkulalliyar kasa.

Buhari ya kuma tabbatar da kurakruran da gwamnatinsa ta yi wajen kula da ‘yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya rutsa da su inda ya ce za a yi cikakken bincike kan game da zargin rashawa na kudaden da aka kebe don Jin dadin ‘yan gudun hijirar tare da Ladaftar da duk wanda aka samu da laifi.

Ya ce nasarar da aka samu wajen fatattakar mayakan Boko Haram daga hedkwatarsu da ke cikin Dajin Sambisa ya bude sabon faifai a tarihin tsaron lafiya a Nijeriya inda ya nemi ‘yan Nijeriya kan su sanya ido kan bakin fuska da suka gani a cikinsu tare kai rahoto ga jami’an tsaro.

A cikin sakon, Buhari ya bayyana cewa shirinsa na ganin cewa Nijeriya na ciyar da kanta, ya fara tasiri musamman yadda a wannan shekarar manoma sun sami amfani Gona mai yawan gaske sannan kuma wasu jihohi sun shiga cikin wasu yarjejeniyoyi da bankuna don samar wa manoman jihohinsu rancen noma mai saukin biya.

A karshe, Shugaba Buhari ya yi wa Al’ummar Nijeriya fatan Alheri na sabuwar shekara

You may also like