Sakon ta’aziyya daga Turkiyya zuwa ga Jamus


Shugaban kasar Turkiyya Erdoğan ya aika rubutattun sakonnin ta’aziyya ga ‘yan uwan Turkawan da suka rasa rayukansu a harin Jamus.

A cikin sakonnin da ya aika wa mahaifan matashiya Can Leyla,Selçuk Kılıç da maidakin Sevda Dağ,Erdoğan ya nuna biakin cikinsa dangane rashin da suka yi.

Baya ga haka ya mika sakon ta’aziyyarsa ga shugabanan kasar jamus Joachim Gauck da kuma daukacin al’umar Jamus tare da fatan Allah ya rahamshi mamatan.

Erdoğan ya la’anci wannan mummunan harin wanda ya zama sanadiyar mutuwar mutane 9 da kuma jikkatar wasu 27.

You may also like