
Asalin hoton, Getty Images
Mohamed Salah na fatan Liverpool za ta koma kan ganiya, bayan doke Everton 2-0 a wasan mako na 23 a Premier League a Anfield ranar Litinin.
A wasan na hamayya na Mersyside Derby, Liverpool ta fara cin kwallo ta hannun Salah a minti na 36 da fara tamaula.
Sabon dan kwallon da ta dauka a Janairu, Cody Gakpo ne ya ci na biyu na farko da ya zura a raga a Liverpool.
Haka kuma kwallon farko da Salah ya ci a Premier League tun bayan 26 ga Disambar 2023, lokacin da ya ci Aston Villa.
Liverpool, wadda aka doke ta karo uku a wasa hudu a bayan nan a Premier League kafin haduwa da Everton ta koma ta tara a teburi da maki 32.
Bayan da Liverpool ta buga wasa 21 a Premier ta hau kan Chelsea kenan, ita kuwa kungiyar Stamford Bridge ta yi kasa zuwa mataki na 10.
Salah wanda ya yi wasa biyar bai ci kwallo ba kafin ranar Talata ya ce fatan da suke yi shine su kare a cikin ‘yan hudun farko a bana, domin su buga Champions League a badi.
Liverpool za ta fafata da Newcastle ranar Asabar a Premier League, kwana uku tsakani ta kece raini da Real Madrid a Champions League.