
Asalin hoton, Getty Images
Lalurar wuce iyaka ta BPD kan kashe soyayya idan ba a yi taka-tsantsan ba
“Lokacin da aka gano ina da lalurar wuce iyaka (BPD), na zaci ba zan iya yin lafiyayyar soyayya ba.”
Irin abin da Mae mai shekara 21 ta ji ke nan a farkon wannan shekarar, lokacin da aka faɗa mata tana ɗuke da cutar wuce iyaka ta borderline personality disorder (BPD) – kuma haka da yawa daga cikin masu cutar ke ji a shafukan sada zumunta.
Maganar BPD na ci gaba da samun gindin zama a shafukan zumunta, kuma Dr Liana Romaniuk, ƙwararriya kan yara da lalurar ƙwaƙwalwa a Jami’ar Edinburgh, na ganin irin yadda matasa ke tunkarar matsalar ke nan saɓanin na zamanin baya.
“Na samu matasa da yawa da ke tambaya ta cewa, ‘zan iya kamuwa da BPD kuwa? Ina ganin ana samun ƙaruwar faɗakarwa kan hakan,” in ji daktan.
Borderline personality disorder (BPD) lalura ce da ke shafar ƙwaƙwalwa kuma ta saka wa mutum rashin natsuwa da sauya yadda mutum ya kamata ya gudanar da mu’amala da sauran jama’a.
Ana kyautata zaton tana shafar duk mutum ɗaya cikin 100 a duniya.
Akasarin masu lalurar sun fuskanci damuwa ko kuma banzatarwa a lokacin da suke yara, abin da ke jawo musu matsala wajen yin soyayya idan sun girma.
Dr Romaniuk ta ce damuwa ba lallai sai a kan abu maras daɗi ba ko kuma an zalince su ba – abubuwan sun ƙunshi kamar iyayensu su rabu, su zama ba a jin tunaninsu, ko kuma mutuwar uwa ko uba lokacin da suke yara.
Asalin hoton, Getty Images
Masu lalurar wuce iyaka na so su dinga yawan kira ko yi wa wanda suke soyayya da shi saƙon tes
Akwai muhawara tsakanin ƙwararru, a cewar Dr Romaniuk, kan ko BPD da gaske lalura ce ko kuma wasu abubuwa da suka faru a baya ne ke haifar da matsalar.
Nuna ‘maita’ a soyayya
Mae ta fara bincike kan BPD saboda ta lura tana zama “mayya” da mai yawan zaƙuwa kan soyayya.
“Na lura alamomin cutar na ƙruwa a tare da ni a harkar soyayyata,” a cewarta bayan an gano cutar a tare da ita a watan Maris na 2021.
“Nan da nan nake zaƙuwa. Zan ji ina so na yi ta kira ko tura saƙon tes, kuma zan ji ina so na keɓe daga ƙawayena – na daina yin abubuwan da nake jin daɗi saboda wannan mutumin.”
Abin da wani bai ɗauka a bakin komai ba, inda yana da matsalar BPD sai ya zama gagarumi.
“Wata rana ina gidan ƙawata lokacin da na ga saƙo daga saurayina kuma kalaman sun girgiza ni – nan take na tattara kayana na ce: ‘Dole ma in tafi’, na wuce gidansa kai-tsaye cikin minti 15.
Asalin hoton, Getty Images
Lalurar BPD kan kashe soyayya
“Na dinga jin gabana yana faɗuwa. A ƙarshe dai lafiyata ƙalau. Sai na koma wajen ƙawata. Abin ya ba ta mamaki, amma ban ci gaba da hira yadda ya dace ba saboda gabana ya ci gaba da faɗuwa.”
Fargabar barin mutum ma kan ta’azzara lamarin. “A ‘yan makonnin da suka wuce a soyayyarmu, na yi ta ɓatawa da samarina ina faɗa musu cewa zan ƙyale su saboda ina yi musu hassada [ta irin son da nake yi musu],” a cewar Mae.
“Idan kuma suka rabu da ni sai in ji ba daɗi, in yi ta kiran su ina kuka, ina yi musu magiya su dawo. Irin wannan abu na da alaƙa da lalurata ta BPD.”
Tun bayan gano cutar, Mae ta fara yin wani magani da ake kira dialectical behavior therapy (DBT) a turancin Ingilishi – wanda mutum ke tattaunawa da ƙwararru don gano yadda ya kamata su dinga saita mu’amalarsu.
Ta kuma fara shan ƙwayoyin rage damuwa. “Yanzu na kan ji dama-dama,” in ji ta.
Asalin hoton, Getty Images
Tattaunawa ta gaskiya ka iya kawo ƙarshen lalurar wuce iyaka
Akasari lalurar kan taso ne saboda tsoron rasa abokin zama.
“Abin da masu lalurar suka faɗa min shi ne akwai yiwuwar mutum ya ɓata da abokinsa kafin abokin ya ɓata da shi,” a cewar Dr Romaniuk.
“Mutum zai iya ƙirƙirar dalilin da zai sa ya katse soyayyarsa da wani ko ya shirya jarrabawa don gane masoyinsa na sonsa…amma masu lalurar na ganin gara su zama cikin shiri a kodayaushe saboda gudun abin da ka iya faruwa.”