Salwantar Da Biliyan 2.3 Na Neman Jefa Gwamnan Binuwai Cikin Tsaka Mai Wuya


Majalisar dokokin jihar Binuwai ta yi barazanar tsige Gwamnan jihar, Samuel Ortom bisa zargin salwantar da Naira Bilyan 2.3 ba tare da amincewar ‘yan majalisar ba.

Rahotanni daga jihar sun nuna cewa Gwamnan ya so ya mamayi ‘yan majalisar inda ya gabatar masu da wani kasafi na musamman wanda ya nemi su amince masa ya kashe wadannan kudade bayan da ya rigaya ya salwantar da su.

Ana dai, zargin Gwamnan da rabewa da rikicin Fulani da makiyaya wajen boye gazawarsa a bangaren gudanar da ayyukan raya kasa ga al’ummar jihar ba ya ga kasa biyan albashin ma’aikatan gwamnati.

You may also like