Sama Da Jam’iyyar PDP Dubu 24,000 Ne Suka Koma APC A Jihar Adamawa



Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya tayi rashin yayanta wadanda yawansu yakai kimanin dubu 24,000 a jihar Adamawa 

Barista Ahmed Ali Gulak shine jagoran wadanda suka baro jam’iyyar adawa ta PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki inda yace “ya zama dole mu dauki tsintsiya su share duk wani wanda baya kashin jihar Adamawa”

Shima dai a nashi bangaren shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Adamawa Alhaji Ibrahim Bilal yace suna maraba da duk wanda ke son ci gaban jihar Adamawa da jam’iyyar APC baki daya. 

Malam Muhammad Habibu dan jam’iyyar APC ne a jihar Adamawa ya kuma shaidawa Zuma Times cewa dama yasan za’a rina domin jam’iyyar PDP ta rasa dubban magoya bayanta a jihar kuma wasu ma na nan tafe a cewar sa.

Zuwa lokacin aiko da wannan rahoton Babu wata sanarwa daga jam’iyyar ta PDP akan wannan batu.

You may also like