Sama Da Masallatai 350 nee Sukai Wa Shugaba Buhari Addu’ar Samun Lafiya Daruruwan mutane sun yi wa shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari addu’a a masallatan Juma’a na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeria.
Limamai a masallatai 350 a garin Maiduguri da Jere da Biu da ma wasu sassan jihar ne suka jagoranci dubban mutane domin yin addu’o’i na mussaman domin nema wa shugaba Muhammadu Buhari lafiya. Gwamnan Jihar, Kashim Shettima ne ya bukaci a yi addu’oin.
Kwamishinan harkokin addini na jihar ta Borno, Mustapha M. Fannarambe ya sa hannu a wata wasika da ta bukaci a tsananta addu’a Allah ya bai wa shugaba Buhari lafiya.

Wasikar ta kuma bukaci shugaban limamai ya sanar da masallatan juma’a sannan ya bukaci ita ma kungiyar kiristoci ta Najeriya ta sanar wa malaman coci-coci a yi irin addu’oin a coci-cocin da ke jihar, a ranar Lahadi.
Musulmai sun yi addu’oin ne domin nuna godiya ga jajircewar gwamantin Buhari wajen yakar kungiyar Boko Haram. Nasarar da gwamnatin ta yi a yakinta da kungiyar Boko Haram ne yasa aka kwato ikon wasu al’ummomin kuma aka samar da kwanciyar hankali a sassan jihar da dama.

Masallatan juma’a 542 ne a jihar Borno amma a halin yanzu an yi kiyasin ana amfani da guda 350 saboda ne kawai.

You may also like