Sama Da Mayakan BokoHaram 240 ne Suka Mika Wuya Ga Sojojin Najeriya. 


Rundunar Sojan Nijeriya ta tabbatar da cewa a halin yanzu akalla mayakan Boko Haram 240 suka mika wuya a kasar Chadi.
Da yake karin haske kan batun, Jami’in Yada Labarai na rundunar, Muhammad Dole ya ce rundunar hadin guiwa na kasashen Chadi, Kamaru, Nijar da Nijeriya ( MNJTF) na ci gaba da kai jerin hare hare a kan sauran mayakan Boko Haram da ke cikin dajin Sambisa.

You may also like