Sama Da Raguna Milyan Suka Yi Kwantai A Jos


Dillalan raguna a Kasuwar Dabbobi ta ‘Yan Shanu da ke Nassarawa Jos, sun sun tabka asara a sakamakon rashin cinikin da suka fuskanta a wannan sallar da ta gabata, a sanadiyyar karancin kudi a hannun jama’a saboda matsin tattalin arzikin kasa.

Binciken da LEADERSHIP Hausa ta yi ya nuna cewa raguna sama da miliyan daya da aka sauke  a kasuwar gabanin sallah sun yi kwantai wanda hakan ya tilasta wa dillan jigilar ragunansu zuwa wasu kasuwanni, wasu kuma suka sake jigilarsu zuwa garuruwan da suka fito.

Da yake zantawa da wakilimmu, shugaban kyan kasuwan, Alhaji Kawu Muhammed ya ce dillalan raguna a kowane lokaci irin wannan sukan fito ne daga Jihohin Jigawa, Gombe, Bauchi Kano, Kaduna da  Shendam cikin jihar, inda suke sauke raguna a kasuwar don neman masu saye.

“Masu sayen su ma suna zuwa ne daga Jihohin Legas, Kwara, Binwai, Nasarawa, Abuja da wansu jihohi na kudancin kasar nan don sayen raguna da shanu da rakuma don yin laiyya da su amma a bana sai ‘yan kalilan suka zo suka sayi raguna a kasuwar.”

Ya ce a bana aka fi sauke raguna a kasuwar saboda zaman lafiyan da aka samu yanzu a jihar kuma farashin dabbobi a kasuwar ya yi sauki a kasuwar idan aka kwatanta da na bara.

Alhaji Muhammed, ya yabawa gwamnan jihar Barista Simon Bako Lalong, da yan majalisar zartaswansa, bisa tsayuwar dakan da sukayi na tabbatarda dorewar zaman lafiyan da aka samu yanzu a jihar.

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, daya daga cikin wadanda suke hidimar sayen ragunan yin laiyya, Alhaji Ja’afar Useini, ya ce kowace shekara yakan sayi ragunan layya nashi da na iyalansa amma a bana shi kawai ya iya saye, duk da yake a bana farashinsu ya yi kasan kana ya gargadi mutane da su daina dora lafin matsin tattalin arzikin kasa a kan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Ita ma a zanatawarta da wakilimmun Hajiya Tawakkaltu Ibrana Abdurrahaman, mataimakiyar sakatariyar Kungiyar mata ta FOMWAN, rashen Jihar Filato, ta koka bisa hauhawar farashin kaya a kasuwanni.

Ta ce a kowace shekara takan sayi ruguna biyu zuwa uku amma a bana da kyar ta samu ta sayi daya saboda tsadar rayuwa.

Ta yi amfani da wannan dama wajen kiran gwmnonin jihohi da su rika biyan ma’aikatansu a kan kari don rage wahalhalun da suke fuskanta a sanadiyar tsadar kayayyaki a kasuwanni.

Kuma ta yaba wa gwamnan jihar Barista Simon Lalong bisa kyakkyawar rawar da gwamnatinsa ke takawa wajen hada kan al’ummar jihar da inganta tattalin arzikin jihar, sannan ta bukaci al’ummar jihar da su bashi kyakkyawan hadin kai da goyon baya don ya sami kwarin guiwar yi wa jihar aiki cikin nasara.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like