Sama da wakilai masu kada kuri’a 2800 ne za su halarci babban taron jam’iyyar PDP


Wakilai sama da 2800 ne za suyi zaɓe a babban zaɓen jam’iyar PDP na kasa da za a yi ranar 9 ga watan Disamba, sakataren yaɗa labaran jam’iyar Dayo Adeyaye,ya bayyana haka.

Da yakewa manema labarai jawabi a ranar Alhamis a sakatariyar uwar jam’iyar bayan kammala taron kwamitin zartarwar Jam’iyar wanda aka shafe a sa’o’i da dama kafin a kammala  a Ofishin jam’iyar dake wadata Plaza.

Adeyeye yace kwamaitin zartarwa ya amince da kunshin mutanen dake cikin kwamitin da zai jagoranci shiryawa zaɓen.

 Da aka tambaye shi sunan wanda zai jagoranci kwamitin, kawai sai yace, ” har sai lokacin da muka fitar da jerin  sunayen, kada kuyi riga malam masallaci.”

Adeyeye wanda tsohon karamin ministan aiyuka ne ya ce INEC ta gargadi yan takarkarun mukamai daban-daban a jam’iyar a da su kaucewa kalaman batanci.

Yace kwamitin zartarwar jam’iyar ya karba kuma ya amince da rahoton zabe da aka gudanar a jihohin Borno, Kwara, Lagos,Adamawa, Kogi, Ogun Anambra da kuma jihar Kebbi kamar yadda aka umarta babban taron jam’iyar wanda bana zaɓen Shugabanni ba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like