A karon farko hukumar kula da masu gudun hijira ta kasa da kasa IOM, ta ce yawan yan gudun hijira da suka rayukansu yayin da suke kokarin ketarawa nahiyar turai sun zarta 4,000.
Hukumar ta IOM ta ce rasa rayukan ya zarta irin wanda aka samu a shekara ta 2015 da kashi 26.
Da yawa daga cikin masu gudun hijirar sun rasa rayukansu ne yayin ketara tekun Mediterranean, yankin arewacin Afirka, dakuma kan iyakokin Syria da Turkiyya, duk a kokarinsu na kwarara nahiyar turai.
Mai magana da yawun Hukumar kula da yan gudun hijirar IOM, Joel Millman, ya ce yawan wadanda suka mutun ya zarta 4.000 bayan samun rahoton mutuwar wasu mutanen guda 33 a gabar teku dake Sabratha a kasar Libiya.
Millman ya ce ana samun karuwar kai hari kan yan gudun hijira da suka fito daga Syria da ke san ketara Turkiyya zuwa kasashen turai, inda ya ce kawo yanzu jami`an kula da shige da ficen Turkiyyan sun harbe yan kasar Syria 64.