Majalisar dinkin duniya ta ce ba za a iya cimma kudurin samar da ilmin furamare da sakandare kyauta ga al’umar duniya nan da tsakiyar karni ba.
A bara ne shugabannin kasashen duniya suka sha alwashin samar da ilmin furamare da sakandare kyauta nan da shekara ta 2030, a karkashin shirin samar da ci gaba mai dorewa, amma wani rahoton MDD ya ce rashin kudi na taka-birki ga wannan kudurin.
Rahoton ya ce sai an ninka kudin da ake bukata har sau shida kafin a cimma wannan muradin.Kazalika rahoton ya yi bayani a kan gibin da ke tsakanin kasashe masu arziki da marasa galihu, yana cewa kasashen da suke da karancin makarantu na fuskantar hadarin fadawa cikin rikici da matsalar mutuwar kananan yara.