An samu bullar Zika a Malesiya


 

 

A karon farko a kasar Malesiya an samu bullar cutar nan ta Zika da sauro ke yadawa, mako guda bayan da makociyar kasar wato Singapore ta bayyana cewar cutar ta bulla a kasarta.

Hukumomi suka ce wata mata mai shekaru 58 ta harbu da wannan cuta a Malesiya bayan da ta koma gida daga wata ziyara da ta kaiwa ‘yarta a Singapore wadda ta kamu da cutar a kwanakin da suka gabata kamar yadda ma’aikatar da ke lura da kiwon lafiya a kasar ta bayyana.

Masu aiko da rahotanni suka ce ya zuwa yanzu da maigidan wannan mata da sauran mutanen da ke zaune da ita ba su kai ga kamuwa da wannan cuta ba amma kuma ana sanya idanu a kansu saboda abinda ka je ya koma. Yanzu haka dai jami’an kiwon lafiya a kasar na fadi-tashi wajen ganin ba a samu bazuwar wannan cuta a kasar ba musamman ma dai yankin da wannan mata da ta harbu ta fito.

You may also like