Kaduna: An Samu Karamar Girgizar Kasa A Jaba


Wata karamar girgizar kasa ta shafi garuruwan Sambang Dagi da Nok da ke karamar hukumar Jaba na jihar Kaduna, lamarin da ya tilasta mazauna garuruwan yin gudun hijira.

Rahotanni sun tabbatar da cewa girgizar kasar ta fara aukuwa ne a kauyen Nok da misalin Karfe hudu na dare. Tuni dai gwamnatin jihar ta dauki matakan gaggawa tare da neman mazauna yankin kan su kwantar da hankularsu.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like